An rufe akasarin filayen jiragen sama a Spain
December 4, 2010Gwamnatin ƙasar Spain ta miƙawa sojojin ƙasar ikon kula da sararin samaniyar ta, biyo yajin aikin da ma'aikatan suka shiga. Ma'aikatan filayen jiragen saman ƙasar, sun shiga yajin aikine tun ajiya a dai-dai lokacin da ɗimbin matafiya ke haramar tafiyar hutun ƙarshen makko, inda aka rufe filiyen jiragen saman ƙasar da yawa, ciki harda da na babban birnin ƙasar wato Madrid. Su dai ma'aikata sun bayyana cewa babu jada baya a wannan matakin da suka ɗauka, yayin da shi kuwa ministan sufurin ƙasar ya bayyana wa manema labarai cewa, wannan yajin aikin an shirya shi ne da nufin yin ɓatanci ga gwamnati mai ci. Ma'aikata dake kula da zirga zirgar jiragen saman ƙasar ta Sapain, sun jima suna tattaunawa da gwamnati kan ƙarin albashi da wasu haƙƙoki.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Muhammed Abubakar