Sudan: Rufe bankunan ajiyar dakarun RSF
May 16, 2023Talla
A cewar kafar yada labarun kasar ta SUNA, wannan sabon hukuncin zai shafi dukacin 'yan rundunar RSF da ke da bankuna a kasar gami da kamfanon i mallakinsu.
A karshen makon da ya gabata ne janar Burhan ya sauya gwamnan babban bankin kasar, ya zuwa yanzu babu tabbacin yadda wannan sabon hukuncin zai shafi rundunar da ma yadda take ci gaba da fito na fito da sojojin gwamnati.
Tun a tsakiyar watan Apirilu ne fada ya barke tsakanin sojojin gwamnati da ke karkashin Abdel Fatah al Burhan da kuma ta rundunar sa kai karkashin Mohamad Hamdan Dagolo.
Majalisar Dinkin Duniya da manyan kasashen duniya na ci gaba da kokarin kawo karshen wannan rikicin da bangarorin masu gaba da juna ke ci gaba da kaura fada.