An rusa gwamnatin kasar Ukraine
September 8, 2005Kungiyar gamayyar turai Eu tayi kira ga shugaba Viktor Yushchenko na Ukraine,daya tabbatar da zaman lafiya tsakanin alummarsa ,bayan ya sanar da rusa gwamnatinsa,dangane da zargin rashawa da cin hanci.
Kakakin kungiyar gamayyar turai Emma Udwin,tace kungiyar na fatan shugaba Yushchenko zai cigaba da tabbatar da doka da oder,ta hanyar samun lumana tsakanin alumma sakamakon rusa gwamnastin.
Tace Shugaban na Ukraine dai ya haye karagar kujerarsa ne ,bias kudurin kawo sauyi cikin harkokin gudanarwa ,ta hanyar yaki da ayyukan rashawa da mulki mai adalci ,kuma har yanzu sunyi imanin cewa gwammanatinsa na tafiya bisa kudurorin daya dauka.
Kungiyar ta Eu dai dai ta kulla dangantaka ta kut da kut da Ukraine ,tun da Yushchenko ya lashe zabe,kan tubalin goyon bayan kasashen yammci sakamakon zanga zangar juyin juya hali a wannan kasa.
A yau alhamis nedai shugaba Viktor Yushchenko na Ukraine ya sanar da rusa gwamnatinsa ,a dasi dai lokacin da gwamnatin ke fuskantar rikici na karuwan rashawa da cin hanci,wanda ya jagoranci ajiye mukaman manyan jamian kasar,batu kuma daya kawo ayar tambaya a dangane da matsayin shugaban wanda yah au wannan karaga sakamakon juyin juya hali.
Tuni dai shugaban na Ukraine ya sanar da nada shugaban wata gunduwa mai masanaantu dake gabashin kasar ,Yury Yekhanurov ,a matsayin mai rikon kwarya kuma wanda yam aye gurbin tsohuwar prime minister Yulia Tymoshenko,wadda ta taka muhimmiyar rawa lokacin zanga zangar juyin juya hali na baran.
Yushchenko yace ya rusa gwamnatin nasa ne saboda rigingimu na cikin gida dake addabarta ya fara taba manufofin gwamnatinsa day a sanya gaba.Yace duk dacewa akwai sabbin fuskoki cikin gwamnati,har yanzu manufofin gwamnati basu sauya ba.
Shugaban Ukraine yace abun takaici ,ace yanzu haka an fara zargin kasar da harkokin rashawa da rashin sanin inda tattalin arzikin kasar ta dosa da suka hadar da sayar da hannayen jari.
Wannan rigima data ritsa da gwamnatin Ukraine dai yazo ne adai dai lokacin da manyan jamian kasar ke cigaba da ajiye mukamansu,dangane da zargin cewa na hannun daman shugaba Yushchenko nada hannu cikin harkokin rashawa da ake zargin gwamnati dasu.
Sakataren majalisar tsaron kasar Petro Poroshenko da aka zarga da azurta kansa da dukiyarsa a wannan makon ,zargi daya karyata ,ya ajiye mukaminsa,ayayinda a hannu guda kuma mataimakin prime minister Mykola Tomenko a taron manema labaru ya sanar dacewa zaiyi yi murabus dangane da harkokin rashawa dake guda a wannan gawamnati data kira kanta,mai adalci da gaskiya .
A jawabinsa na jiya dai Shugaba Yushchenko ya sanar da gudanar da bincike cikin harkokin rashawa da ake zargin gwamnatinsa da tabkawa.To sai dai jim kadan da wadannan kalamai nasa a jiyan ,shugaban hukumar tsaro na kasar Olexander Turchinov ya sanar da ajiye mukaminsa.Ana dai ganin cewa yin murabus na wannan jammiin bazai kasa nasaba da kusantakarsa da Priministan kasar da aka sauke ba.