An yi garkuwa da Bajamushe limamin coci a Mali
November 21, 2022Talla
Wasu da ake zargin masu kaifin kishin addini sun yi garkuwa da wani limamin coci dan kasar Jamus a Bamako babban birnin kasar Mali, Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 10 da aka sace wani dan kasar yammacin duniya a Mali.
Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin yin garkuwa da limamin cocin, wanda ya shafe fiye da shekaru 30 a Mali, sai dai tuni aka dora zargi kan kungiyar IS mai tarihin garkuwa da 'yan kasashen waje don samun kudin fansa.