An saci bayanan sirrin miliyoyin mutane a Facebook
April 4, 2021Talla
Shafin Business Insider a yanar gizo ya fara bankado yadda masu kutsen suka saci bayanan mutane daga kasashe 106, ciki har da lambobin waya da cikakkun suna da tushen shafukan Facebook da wuri da bayanan haihuwa da adireshin email na mutane sama da miliyan 500.
Kamfanin Facebook na cikin mastala na rashin iya kare bayanan sirri na masu amfani da shafin, inda a shekarar 2018 Facebook din ta soke damar neman bayanan mutane ta amfani da lambar waya, bayan da kamfanin Cambridge Analytica ya saci bayanan mutane miliyan 87 a Facebook ba tare da saninsu ko yardarsu ba.