1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

An saka ranar zaben shugaban Rasha

Suleiman Babayo ZMA
December 7, 2023

Za gudanar da zaben shugaban kasar Rasha cikin watan Maris na shekara mai zuwa ta 2024, inda ake sa ran Shugaba Vladimir Putin zai neman sbaon wa'adin mulki na shekaru shida.

https://p.dw.com/p/4ZtqL
Shugaba Vladimir Putin na Rasha
Shugaba Vladimir Putin na RashaHoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Majalisar dattawa ta kasar Rasha da ke zama majalisar shawara ta amince da saka ranar 17 ga watan Maris na shekara mai zuwa ta 2024 a matsyin ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasar. Ana sa ran Shugaba Vladimir Putin zai ayyana takara kan sake neman mukamun na shugaban kasar. Idan Putin mai shekaru 71 ya samu nasara a zaben mai zuwa zai mulki kasar har zuwa shekara ta 2030 kuma yana da izinin sake takara domin ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2036.

A wani labarin Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yaba bisa dangantakar da ke wakana tsakanin kasarsa da kuma Iran, inda ya bayyana hakan lokacin da yake karban bakuncin Shugaba Ebrahim Raisi na kasar Iran. Shugabannin biyu sun kuma tattauna rikicin da ke faruwa tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu.