An sake dawo da kullen corona a Jamus
October 28, 2020Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da gwamnonin jihohin kasar, sun amince da amfani da kadaden da suka kai Euro biliyan 10 domin bai wa kamfanonin da za a tilasta wa rufe harkokinsu sakamakon sabbin matakan kulle da aka tsara dauka saboda hana yaduwar cutar corona a kasar.
Kanana da matsakaitan kamfanoni za su samu 75% na asarar da za su iya tafkawa cikin watan Nuwamba, yayin da manyan kamfanonin Jamus din za su sami 70%.
Hukumomin na Jamus sun ce za a rufe wuraren al'adu da na shakatawa da gidajen abinci da shagunan barasa, matakin da zai fara aiki a ranar Litinin da ke tafe.
Wasu shaguna musamman na bukatun yau da kullum za su ci gaba da kasancewa a bude, sai dai karkashin tsauraran matakan tazara tsakanin jama'a.
Su ma makarantu an amince da ci gaba da koyo da koyarwa a cikinsu, sai dai za a kara matakan tsaftace jiki lokaci zuwa lokaci.
Shagunan kwalliya da zaurukan tausa za su kansace a garkame tsawon makonni hudun da ke tafe, a cewar mahukuntan kamar yadda su ma wasannin Lig-Lig na Jamus wato Bundesliga, za su kasance babu 'yan kallo.