An sake gangami kan Shugaba Barrow
January 13, 2020Dubban 'yan kasar Gambiya ne suka mamaye manyan hanyoyin Banjul, inda suke ta kiraye-kirayen Shugaba Adama Barrow da ya yi mulkin shekaru biyar, maimakon uku da ya alkawarta a shekara ta 2016.
Sabon macin Gambiyawan ya zo ne bayan wani da wasu 'yan kasar suka yi cikin watan Disamba, inda su kuwa suke bukatar shugaban da kada ya wuce shekarun uku, da ya debar wa kansa.
Shi dai Shugaba Adama Barrow, ya sanya hannu kan yarjejeniyar cewar zai kasance ne shugaba da zai mika mulki ga wata sabuwar gwamnati, bayan kawo karshen shugabancin tsohon Shugaba Yahya Jammeh.
A share guda kuwa tsohon Shugaba Jammeh, wanda a halin yanzu ke zaman hijira a kasar Equatorial Guinea, ya nuna bukatar a kyale shi da ya koma gida.
Tsawon shekaru 22 ne dai tsohon shugaban ya mulki Gambiya, inda ya sauka bayan matsin lamba daga kasashen duniya.