An sake kama Bobi Wine
March 15, 2021Talla
Jawabin da aka wallafa a shafin offishinsa na twitter na nuna cewa Bobi Wine ya jagoranci ‘yan majalisar da sauran shugabanni don nuna adawa ga garkuwa da azabtarwa da kuma kisan magoya bayansa a birnin Kampala.
Rahotannin dai na nuna cewa mahukuntan Yaganda na zargin Wine da yunkurin kawo karshen gwamnatin shugaba Yoweri Museveni ta hanyar zanga-zanga.Tun dai a ranar 10 ga wannan Maris ne dai Bobi Wine ya ce kwanaki 70 kenan da hukumomi a kasar suka kame tawagar masu gangamin goya masa baya a Kalangala.
Jagoran adawan dai ya kasance a tsare a gida a watan Janairun da ya gabata yayin da ya ke kalubalantar sakamakon zaben inda daga baya wata kotu a kasar ta yanke hukunci dangane da kamen nasa.