An sako dan jaridar Al Jazeera a Jamus
June 22, 2015Talla
Tashar telebijin ta Al Jazeera ta ce mahukunta a Jamus sun sako dan jaridarta da aka kamae Ahmed Manusr. Tashar ta ce mai gabar da kara na Jamus ya yanke shawarar sakin Manusr ba da an tuhumeshi ba, amma kuma ba a yi karin bayani ba. Da farko ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce kasar ba za ta tsa keyar wani zuwa wata kasa inda yake fuskantar hukuncin kisa ba. A ranar Asabar aka kame Ahmed Mansur a filin jirgin saman birnin Berlin bisa wata bukata daga kasar Masar.