An sako 'yan Tunusiya da aka sace a Libiya
June 19, 2015A kasar Libiya a yau juma'a an sako jami'an diplomasiyyar nan na Kasar Tunusiya su goma wadanda kungiyar wasu tsageru na kasar ta Libiya ta sace a makon da ya gabata a birnin Tripoli.Ministan kula da harakokin kasashen wajen Kasar ta Tunisiya Taieb Bakouch ne ya tabbatar da wanann labari a ranar juma'a.
Babu dai wani bayani da Ministan ya yi a game da yanayi ko kuma sharadin da aka karbo mutanan daga hannun wadanda suka sace su ,amma dai sakin mutanan ya biyo bayan matakin da kotun Kasar Tunusiyan ta dauka na mika Walid Kalib mamba a wata kungiyar 'yan bindiga ta Kasar Libiya mai suna Aube Libiyenne wace ta kori halitacciyar gwamnatin kasar daga birnin Tripoli.
Ministan kasar ta Tunisiya ya ce dai tuni mutanan da aka sako suka isa birnin Tunis.Sannan ya ce kasarsa ta dakatar da huldar diplomasiyyarta da Kasar ta Libiya bayan abkuwar wannan lamari.