Senegal ta sallami tsohon shugaban Chadi daga gidan yari
April 7, 2020Talla
Tun daga farko dai kotun kasar ta Senegal inda tsohon shugaban kasar ta Chadi yake tsare, ta ce lauyan da ke kare Hissène Habré ya shigar da wata bukatar bayar da belinsa a gabanta, duba da yanayinsa na shekaru da kuma yadda yake iya harbuwa da kwayar cutar Coronavirus a gidan yarin da yake tsare a birnin Dakar, bukatar da kuma ta amince da ita. Mai shekaru 78 a duniya Hissène Habre, A wani zamanta na musamman a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2016, kotu ta kama shi da laifin aikata kisan kiyashi ne a kasar Chadi bayan ya yi mulki irin na kama karya a shekaru 1982 zuwa 1990, inda ake zargin mutane fiye da dubu 40 sun hallaka.