An tabbatar da laifin amfani da makami mai guba
January 27, 2023Hukumar da ke sa ido kan makamin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakin harin da aka kai da sinadarin chlorine da ya hallaka mutum akalla 43 a Siriya kan rundunar sojin kasar bisa umarnin Shugaba Bashar al-Assad. Masu binciken sun ce, akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da yadda rundunar sojin saman Siriya ta jefa wasu tukwanen gas biyu da ke kunshe da sinadarin mai guba kan tungar 'yan tawaye a yankin Douma a shekarar 2018 da ake tsakiyar yakin basasar Siriya.
Fararen hula na daga cikin wadanda suka salwanta a kazamin harin. Yanzu dai ana ganin wannnan zai kawo karshen gardamar da aka jima ana yi a tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da wasu manyan kasashen yamma da suka zargi gwamnatin Damascus da aminiyarta Rasha da hannu a harin.
Shugaba Bashar al-Assad ya sha musanta zargin amfani da makami mai guba da Majalisar Dinkin Duniya ta haramta, a yayin da Rasha ta ce, 'yan tawayen ne suka haifar da harin a sakamakon fashewar tukwanen na makamai masu guba da suka boye, mutum sama da dubu daya da dari hudu ne suka mutu bayan shakar sinadari mai guba a tsawon lokacin da aka kwashe ana gwabza fada a Siriya.