1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sanar da ranar jana'izar Sarauniya Elizabeth ta II

September 10, 2022

Masarautar Birtaniya ta sanar da ranar da za a yi jana'aizar Sarauniya Elizabeth ta II, wadda ta rasu a ranar Alhamis. A yau ne kuma Sarki Charles ya kama ragama.

https://p.dw.com/p/4Gg4j
Großbritannien | Tod Queen Elizabeth | Kondolenzbücher
Hoto: Matthew Horwood/Getty Images

Rahotanni daga fadar Buckingham ta Burtaniya, na cewa za a yi jana'izar marigayiya Sarauniya Elizabeth ta II a ranar 19 ga wannan wata na Satumba da muke ciki a Westminster Abbey da ke birnin London. Za dai a binne sarauniyar ne, bayan an bai wa al'umma damar yin bankwana da gawarta.

Sarauniya Elizabeth ta II ta kasance Sarauniya mafi dadewa a kan karaga a tarihi, kuma ta rasu ne tana da shekaru 96 a duniya bayan ta kwashe tsawon shekaru 70 tana mulki.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai, sarauniyar ta riga mu gidan gaskiya a gidanta da take hutun bazara a Balmoral da ke Scotland.

Tuni dai aka yi bikin rantsar da babban danta Sarki Charles na III a matsayin sabon Sarki a fadar ta Buckingham, bikin da ke zaman matakin farko na bayyana sabon sarki a Birtaniya.