An sha arangama a Kataloniya
October 1, 2017Talla
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Kataloniya Carles Puigdemont ya ce abin takaici ne abin da jami'an tsaro suka yi a kan masu zaben. Ya ce: ''Amfani da karfin da ya wuce kima da gwamnatin Spain ta yi, ba zai hanna al'ummar Kataloniya ba yin zabe cikin ruwan sanhi don demokaradiyya ta tabbata. Kawo yanzu dai mutane 38 suka jikkata a taho mu gaman, yayin da jami'an tsaro 11 suka samu raunika.