An shekare da ayyana Corona a matsayin annoba
March 11, 2021Talla
Bullar cutar Coronavirus a duniya, ba kawai tattalin arziki da bil adama ba ne ta yi wa illa, hatta yunkurin alkinta mahalli ma ba a bar shi a baya ba, in ji wani rahoto da kungiyar alkinta mahalli ta kasa da kasa ta fitar a wata mujalla.
Bayanan hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika shekara guda cur da ayyana cutar a matsayin annoba.
Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ce ta ayyana cutar ta Corona a matsayin annoba a shekarar bara ta 2020, bayan da aka fara samun bullarta a birnin Wuhan na kasar Sin.
Sai dai wani bincike da masana suka yi a 'yan makwannin da suka gabata, sakamakon farko-farko na nuni da cewa ba a Wuhan ba ne cutar ta samo asali.