1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An shirya bude taron sulhun Masar kan yakin Gaza

April 28, 2024

Wani babban jami'in kungiyar Hamas ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa kungiyar za ta gabatar da daftarin bukatarta na tsagaita bude wuta a Gaza a zaman da zasu yi a Masar.

https://p.dw.com/p/4fGw0
Birnin Jabalia da dakarun Isra'ila ta shafe a Gaza
Birnin Jabalia da dakarun Isra'ila ta shafe a GazaHoto: Mahmoud Issa/REUTERS

Jami'in wanda ya nemi a sakaye sunansa ya ce kungiyar za ta isa kasar Masar a karkashin jagorancin Khalil al-Hayya, inda zai gabatar da bayanai kan bukatar da Isra'ila ta gabatar na tsagaita wuta da musayar fursunoni.

Karin bayani: Guterres: Gabas ta Tsakiya ka iya fadawa yaki

An dai shiga wata na bakwai a luguden wutan da Isra'ila ke yi a yankin Gaza da zummur murkushe mayakan Hamas da suka kai mata hari a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda yayi sanadiyyar mutuwar al'ummar Isra'ilan 1,200.

Karin bayani: Isra'ila za ta shiga sulhun Masar bayan kashe jami'an jinkai

Hare-haren na Isra'ila na fatattakar kungiyar ta Hamas ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa sama da 34,000 a cewar ma'aikatar lafiyar Gaza.