SiyasaAfirka
Kamaru: 'Yan gudun hijira 18 sun mutu a harin ta'addanci
August 5, 2020Talla
An tura wata tawaga ta jami'an aikin ceto zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Arewacin kasar Kamaru, bayan wani hari da aka kai da ya yi sanadiyyar rayukan 'yan gudun hijira kimanin 18.
Wani mai magana da yawun Hukumar kula da 'yan gudin hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) Babar Baloch, ya fada ma taron manema labarai a birnin Geneva cewa, hukumar na zargin mayakan Boko Haram da hannu a harin na ranar Lahadin da ta gabata.
Jami'in ya kara da cewa, tun daga watan Yuli, ake samun karuwar hare-hare daga mayakan kungiyar ta Boko Haram da wasu kungiyoyi na masu gwagwarmaya da makamai a yankin da ke iyaka da tarayyar Najeriya.