1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soma zaman makoki bayan hari a Masar

November 25, 2017

Al'ummar kasar Masar ta soma zaman makoki na kwanaki uku daga wannan Asabar din domin juyayin mutanen da suka rasu mumunan harin ta'addanci da aka kai wani masallaci

https://p.dw.com/p/2oF9k
Ägypten Sinai Al Arish Anschlag auf Rawda Moschee
Hoto: picture-alliance/AA

Rundunar sojojin kasar Masar ta ayyana kai hare-hare a wuraren da ake gani na 'yan ta'addan ne, sai dai kuma masharhanta sun yi tsokaci kan wannan lamari inda a cewar Reda Mahmoud na cibiyar kula da yaki da ta'addanci a kasar ta Masar wannan harin wani yunkuri ne na haddasa rudani:

"Na farko dai su 'yan ta'addan na kai hari ne ga wuraren ibada, domin sun kai hari a Mujami'u, yanzu kuma sun kai wani harin cikin Masallaci, don haka burinsu shi ne haddasa rikici tsakanin adinai musamman ma na Kristoci da Musulmi, suna so ne su wargaza yardan da al'ummar kasar Masar take bai wa tsarin samar da tsaro a kasar."

Harin na ranar Juma'a dai ya wakana ne yayin da jama'a ke tsakiyar sallar Juma'a a masallacin Al-Rawda da ke birnin Al-Abed mai nisan kilomita 40 a yammacin Al-Arish, babban birnin jihar arewacin Sinaï. Shugaban kasar ta Masar dai ya sha Alwashin mayar da martani mai tsanani kan wadanda suka kai wannan hari. Sai dai kuma babu wanda ya dauki alhakin kai harin.