1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabbatar da Ban Ki Moon a matsayin magajin Kofi Annan

October 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bug2
Kasashe 192 membobin babbar mashawartar MDD a hukumance sun amince da mi nistan harkokin wajen KTK Ban Ki-Moon a matsayin sabon babban sakataren majalisar ta dinkin duniya. Yanzu haka dai Ban zai gaji Kofi Annan wanda zai sauka daga wannan mukami a karshen watan desamba bayan ya shafe shekaru 10 a matsayin babban sakataren MDD. Ban mai shekaru 62 a duniya wanda kwararren jami´in diplomasiya ne ya ce zai yi amfani da halayya ta kara da aka san ´yan Asiya da ita wajen jagorantar gamaiyar ta kasa da kasa amma yayi kashedin cewa ka da a dauki hakan tamkar gazawa. Shi zai kasance babban sakataren MDD na 8 tun bayan kafa ta a shekarar 1945 kuma shi ne dan Asiya na biyu da ya taba rike wannan mukami.