1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tarwatsa masu zanga-zanga a Thailand

August 7, 2021

'Yan sandan kwantar da tarzoma a Thailand sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar neman Firanminista Prayuth Chan-Ochan ya sauka daga mukaminsa sakamakon gazawa da ya yi.

https://p.dw.com/p/3yhAE
Thailand | Proteste gegen die Regierung in Bangkok
Hoto: Lauren DeCicca/Getty Images

Masu zanga-zangar a birnin Bagkok wadanda yawancin su matasa ne da dalibai na neman firanministan Thailand Prayuth Chan-Ochan ya sauka daga mukaminsa saboda rashin amincewa da salon yadda yake yakar annoba corona da ma mummunan halin da tatattalin arzikin kasar ke ciki.

Firanministan na Thailand mai shekaru 67 da haihuwa, wanda kuma tsohun hafsan soji ne ya fuskanci makamanciyar wannan zanga-zanga a makonnin da suka gabata; inda masu sukar lamirinsa ke ikrarin cewa ya karkatar da kudin da ke shiga masarautar da kuma fannin dakaru zuwa ga yaki da annobar Covid-19.

Mahukunta sun bayar da rahoton sabon adadin masu dauke da cutar a wannan Asabar (07.08.21) inda suka ce sun kai kimanin mutum 22,000 yayin da aka samu karin mutum 212 da suka mutu a Thailand sakamakon kamuwa da corona.