An tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Gaza a Turkiyya
November 6, 2023'Yan sandan kasar Turkiyya sun tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kusa da sansanin sojin Amurka da ke Ankara babban birni kasar, sa'o'i kalilan kafin saukar sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a kasar don fara ziyarar aiki a yau, inda zai gana da ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan a gobe litinin.
Karin bayanAsibitoci da dama sun rufe a Zirin Gazai:
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa 'yan sandan sun tarwatsa masu zanga-zangar lumanar da ruwan zafi, bayan da suka fara tunkarar sansanin sojin Amurkan, ko da ya ke babu rahoton kama kowa ko kuma jin rauni daga masu zanga-zangar.
A gefe guda kuma a yau din dai mutane kusan dubu guda sun gudanar da wata zanga-zanga a bakin harabar ofishin jakadancin Amurka da ke birnin na Ankara.
Karin bayani:Guterres ya bayyana damuwa kan kisan mutane a Gaza
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha fitowa fili karara yana nuna goyon bayansa ga Falasdinawa.