An tashi taron ministocin kudi na G20 baram-baram
March 1, 2024Talla
Ministan kudi na kasar Brazil mai masaukin baki, Fernando Haddad ya bayyanawa manema labarai cewar rarrabuwar kawunan da aka samu a tsakanin mambobin na G20 na da nasaba da taron da ministocin harkokin kasashen ketare na G2 da ya gudana a makon jiya, wanda suka tattauna batun rikicin yankunan.
Kungiyar ta G20 ta tafka mahawara a kan yadda za ta kira ci gaba da mamayar Rasha a Ukraine da murya daya.
A cewar mataimakin ministan kudi na kasar Japan, rikici na da mumunar illa ga tattalin arzikin duniya, wanda yanzu haka halin da ake ciki ya shafi farashin makamashi da na abinci da ma sauransu.
Taron dai ya kammala ne ba tare da cimma wata kwakwarar matsaya ta bai daya ba, wanda kuma hakan ba shi ne karon farko a tarihin kungiyar ba.