1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tattauna akan shirin nukiliyar Iran

February 27, 2013

Kasashen mambobin Majalisar Dinkin dDuniya da ke da ikon hawa kujerar na ki sun kawo karshen tataunawar tare da Iran a game da shirinta na nukiliya da ake takaddama akai, a birnin Almaty na kasar Kazakhstan

https://p.dw.com/p/17miE
Hoto: Reuters

Dukkan bangarorin sun daidata kan ci gaba da tattaunawa a farkon watan Afrilu. To amma gabanin haka akwai wani zama da aka shirya kwararru za su gudanar akan wannan batu a watan Maris a birnin Istanbul na kasar Turkiya. Babban mashwarcin Iran, Said Jalili ya nuna gamusuwarsa game da yadda tattaunawar ta gudana. Jalili ya ce a halin yanzu ana samun kusantar juna a dangane da shawarwarin da sauran bangarorin da ke cikin tattaunawar suka gabatar da wadanda ita kanta Iran ta gabatar.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Riabkov ya tabbatar da labarin da kamfanin dillacin labarun Interfax ya bayar cewa bangarorin sun yi wa Iran tayin sassauta takunkumin da aka kakaba mata in har ta yarda ta dakatar da shirnta na bunkasa sinadirin Uraniumn a tasharta nukiliyarta da ke garin Fordo. To sai dai kasar mai bin tsarin Islama ta sa kafa ta haure wannan tayi.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu