Senegal:An tsare Ousmane Sonko a gidan yari
July 31, 2023Talla
An dai kama madugun adawar ne bayan wani artabu da jami'an tsaro a kofar gidansa.
Masu gabatar da kara sun ce laifukan da ake tuhumarsa da su sun biyo bayan kalaman da ya furta ne da taruka da ya gudanar da kuma wasu abubuwan da suka faru tun shekarar 2021.
Dan adawar wanda ya yi kaurin suna wajen sukar shugaban kasa Macky Sall ya ci gaba da yajin cin abinci kwana guda bayan kama shi.
Ministan cikin gida na kasar Senegal ya ce an soke Jam'iyyar Pastef ta Sonko sakamakon yawan kiran da ya ke yi na tunzura jama'a su yi bore abin da ya kai ga haifar da ta'asa da kuma hasarar rayuka.
Ana dai fargabar matakin na iya haifar da sabon tashin hankali a fadin kasar ta yammacin Afirka