An tsawaita yarjejeniyar fitar da hatsin Ukraine
May 18, 2023Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyib Erdogan ne da kansa ya sanar da sake tsawaita yarjejeniyar mai mahinmanci bisa amincewar Rasha da Ukraine. Tuni dai mataimakin firaministan Ukraine Oleksandre Koubrakov de ke bin diddigin yarjejeniyar ya yaba da matakin yana mai gode wa Majalisar Dinikin Duniya da kuma Turkiyya bisa kokarin da suke don kauce wa duniya barazanar karancin abinci.
Suma dai a nasu bangare, hukumomin Rasha sun tabbatar da tsawaita wa'adin yarjejeniyar suna masu korafin rashin daidaito na hana mata fitar da kaya karkashin yarjejeniyar sabili da takunkumai da kasashen Yamma suka kakaba mata. Sai dai masharhanta na kallon amincewa da Rasha ta yi da tsawaita yarjejeniyar a matsayin wani kokarin da shugaba Vladimir Putin ke yi na kama wa abokinsa Recep Tayyib Erdogan da ke neman wani wa'adin mulki a zaben kasar zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 28 ga watan Mayu.