An tuhumi Firamistan Pakistan da raina kotu
February 13, 2012Talla
Kotun ƙolin Pakistan a yau litinin ta tuhumi Firaministan ƙasar Yousuf Raza Gilani da laifin raina kotu bisa ƙememe da ya yi wajen sake buɗe zargin cin hanci da ake yiwa shugaban ƙasar Asif Ali Zardari. Idan aka tabbatar da laifin da ake tuhumarsa da aikatawa Firaminista Raza Gilani ka iya fuskantar ɗaurin watanni shida a gidan yari da kuma tilasta masa sauka daga muƙaminsa. Ƙarar wadda ta haifar da rashin jituwa tsakanin shugabannin farar hular da ɓangaren shari'a akwai yiwuwar za'a ɗauki tsawon lokaci ana tataɓurza akanta. Bayan da ya baiyana a kotun Firaministan Yousouf Raza Gilani ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh