Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya shawarci wasu kasashe
May 20, 2020Talla
Ya kuma kara da cewar annobar ta COVID-19 ba ta yi mummunar illa a nahiyar Afirka ba kamar yadda masana lafiya suka yi hasashe tun farkon billar ta, don haka ya zama wajibi zauren Majalisar Dinkin Duniya ya godewa da dama daga cikin kasashen na Afirka da kungiyoyi sakamakon jajircewa a fagen yaki da cutar da ta haifar da tsaiko a bangaren Ilimin da tattalin arziki.
Kasa da mutane 3000 ne suka rasa rayukansu daga cikin mutane 88,000 da suka kamu da cutar corona a nahiyar Afirka, adadi mafi karanci cikin mutane dubu dari 320 da suka mutu a fadin duniya sakamakon kamuwa da annobar ta COVID-19.
Antonio Guterres ya jaddada bukatar saukakawa kasashe masu karamin karfi hanyoyin biyan bashi.