An yanke hukuncin kisa ga wasu fursuna a Masar
February 2, 2015Talla
Kotun ta ce ta samu mutanen da laifin taka rawa a lokacin da masu bore suka kashe wasu 'yan sanda guda 11 da wasu farar hula guda biyu,a Kerdassa da ke a yammacin birnin Alƙahira a cikin watan Augusta na shekara ta 2013.
A lokacin zanga-zanga da ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatin Mohammed Morsi a cikin watan Yuli na shekarar ta 2013. A halin da ake ciki kuma wata kotun a ƙasar ta Masar ta sanar da cewar nan gaba a ranar 15 ga wannan wata. Za a sake gurfanar da tsohon shugaban ƙasar Mohammed Morsi a gaban ƙuliya a karo na fuɗu a kan laifin cin amanar ƙasa da kuma leƙen asiri.