1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yanke wa sojan Rasha hukunci a Ukraine

May 24, 2022

Wata kotu a Ukraine ta yanke wa wani jami'in sojin Rasha hukuncin daurin rai da rai bisa laifin kashe wani farar hula.

https://p.dw.com/p/4Blte
Ukraine I Prozess gegen Vadim Shishimarin
Hoto: Natacha Pisarenko/AP Photo/picture alliance

A shari'ar da ke kasancewa ta farko a Ukraine da ta danganci yakin kasar, an yanke wa Sajan Vadim Shishimarin mai kimanin shekaru 21 da haihuwa hukuncin ne bisa laifin harbe wani tsohon mai kimanin shekaru 62 a yankin Sumy a lokacin da ake yaki. Sai dai kuma lauyan da ke kare shi da Ukraine din ta nada na cewa za su daukaka kara.

Masu gabatar da kara a Ukraine dai na bincike kan dubban laifukan yaki da aka aikata a kasar da suka hada da harin bam da aka kai wani gidan shakatawa da kuma asibitin yara a kasar da ma kaburburan da aka gano a garin Bucha, makwanni biyu bayan da dakarun Rasha suka janye daga birnin Kyiv.

Tuni ita ma Rashar ta ce ta yiwu ta fara gurfanar da dakarun Ukraine da suka mika wuya a ma'aikatar sarrafa karafar kasar ta Azovstal.