SiyasaAfirka
'Yan bindiga sun saci mutum sama da 50 a Sokoto
June 12, 2022Talla
A Najeriya, sama da mutane 50 ne 'yan bindiga suka kwasa a tsakanin jihohin Sokoto da Zamfara. Bayanan da DW ta tattaro na nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar da yammaci, a lokacin da mutanen 'yan jihar Zamfara ke kokarin komawa gida Gusau bayan halartar wani daurin aure a garin Tambuwal.
Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun yi nasarar kwasar mutanen a tsakanin karamar hukumar Tureta da ke jihar Sokoto da Bakura da ke jihar Zamfara. To sai dai rahotanni na cewa wasu daga cikin mutanen da 'yan bindigar suka kwasa sun kubuta daga hannun maharan da suka addabi jihohin arewa maso yammacin Najeriya.