Masar: Jana'izar Kiristocin da aka kashe a harin ta'addanci
April 10, 2017Masarawa mabiya addinin Kirista a wannan Litinin sun yi jana'izar 'yan uwansu, kwana guda bayan halaka akalla mutane 44 a wasu tagwayen hare-haren bam na kunar bakin wake da aka kai kan wasu majami'u biyu a wasu birane biyu na kasar lokacin bikin Palm Sunday daya daga cikin bukukuwan gabatowar bikin Easter.
Mata sun yi ta kuka lokacin da aka kai akwatunan daukar gawa a cocin Mar Amina da ke a birnin Askandariyya da ke gabar teku. Malaman cocin Kifdawa da masu makoki rike da furanni sun shiga cikin jerin masu jana'izar a cocin.
Akalla mutane 17 aka kashe a majami'ar St. Mark da ke a birnin na Askandariyya da ke zama cibiyar tarihi ta addinin Kirista a Masar. Sannan akalla mutane 27 suka mutu a daya harin da aka kai a majami'ar St. Geirge da ke a birnin Tanta.
Shugaban Masar Abdel-Fatah el-Sissi ya ayyana dokar ta-baci a fadin kasar a daidai lokacin kungiyar ta'adda ta IS ke karkata hare-harenta kan farar hula musamman ma Kiristoci da ke zama tsiraru a Masar.