1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta halaka mutane a Borno

Ahmed Salisu LMJ
November 29, 2020

Gwamnan jihar Borno da ke Najeriya Babagana Umara Zulum ya jagoranci al'ummar kauyen Zabarmari da ke karamar hukumar Jere, wajen yin jana'izar mutanen nan 43 da aka kashe.

https://p.dw.com/p/3lyrV
Afrika Nigeria Borno Professor Babagana Umara Zulum
Gwamnan jihar Borno Farafesa Babagana Umara Zulum Hoto: Government House, Maiduguri, Borno State

'Yan kauyen da dama gami da jami'an gwamnati ne dai suka halarci wannan jana'iza ta mutanen wandanda hallaka ta hanyar yi musu yankan rago. Ya zuwa yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki alhakin wannan danye aiki, sai dai sau da dama kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a kasar, ta saba kai irin wannan hari. Tuni dai shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan da aka yi a wani sako da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fidda ta shafinsa na Twitter a daren Asabar.

Su kuwa al'ummar kasar, musamman ma na arewaci cigaba suke yi da nuna rashin jin dadinsu kan yadda lamuran tsaro ke cigaba da tabarbarewa a yankin nasu, inda suka yi kira ga gwamnati da ta yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin ta kawo karshen kashe-kashe da kuma sace-sacen mutane da ake yi don neman kudin fansa. A hannu guda kuma, wata sanarwa da ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bayar ad agaji ya fitar, ya nunar da cewa sama da mutane 100 ne 'yan ta'addan suka halaka. Sanarwar ta bayyana kisan da mafi muni a wannan shekara, inda ta bukaci gwamnatin tarayya ta tabbabar an hukunta wadanda su ka yi wannan aika-aika.