1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi karin kudin man fetur a Zimbabuwe

Ahmed Salisu
January 13, 2019

Shugaban Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa ya sanar da karin farashin man fetur a kasar, daidai lokacin da al'umma ke kokawa da karancinsa da ake fusakanta a sassan kasar daban-daban.

https://p.dw.com/p/3BUAu
Simbabwe Victoria Falls Tankstelle, ausverkauft
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Shugaban ya ce ya dau wannan mataki ne don ganin an samu sauki kan karancin man fetur din da ake fuskanta sai dai bai yi karin haske ba kan yadda ya ke ganin hakan zai taimaka wajen samun man fetur din a kasar.

Sanarwar ta shugaban ta zo ne sa'o'i kalilan kafin barinsa Zimbabuwe zuwa wasu kasashen duniya ciki kuwa har da Rasha don neman 'yan kasuwar da za su zuba jari a kasar, kafin daga bisani ya karkare ziyarar kasashen ketare din da halartar taron tattalin arziki na duniya a birnin Davos na kasar Switzerland.