An yi kira da a kara azama a kan rikicin bashin kasar Girika
March 19, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga dukkan bangarorin da rikicin basussukan kasar Girika ya shafa da su kara zage dantse wajen samun maslaha. Merkel ta fada wa majalisar dokokin Bundestag a birnin Berlin cewa ana bukatar hadin guiwa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki a batun bashin na Girika. Ta yi kashedin cewa idan tsarin takardun kudin bai daya na Euro ya ruguje to nahiyar Turai ma za ta ruguje. A wannan Alhamis shugabannin kasashe da na gwamnatocin kasashen tarayyar Turai za su yi taron kolin yini biyu a birnin Brussels, taron da rikicin kudin kasar Girika ya mamayen ajandarsa. A gefen taron kuma Firaministan Girika Alexis Tsipras zai yi wata haduwa ta musamman da Angela Merkel da shugaban Faransa Francois Holland da kuma manyan wakilan hukumomin kungiyar EU.