An yi kira da sanya adadin 'yan cirani ga EU
April 29, 2015Sakamakon mace-macen 'yan cirani a tekun Bahar Rum, shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya yi kira da samar da wata doka da za ta tilasta wa daidaikun kasashen EU daukan wani kaso na 'yan cirani. Juncker ya fada wa majalisar Turai da ke birnin Strassburg cewa a ranar 13 ga watan Mayu mai kamawa hukumarsa za ta gabatar da daftarin dokar. Ya kuma ce za a rubanya kudaden aikin ceto a tekun Bahar Rum.
Juncker ya kara da cewa kasar Italiya ita kadai ba za ta iya samar da kudin tafiyar da aikin ceto a Bahar Rum ba, dole daga yanzu a yi amfani da kasafin kudin Turai da karo-karo na kasashe membobi ga wannan aiki.
Juncker ya yi kuma kira ga kasashen EU da su rubanya taimakon raya kasashe masu tasowa don yaki da musabbabin yin hijirar.