An yi kira ga Iran da ta amince da tayin da aka yi mata
June 3, 2006Talla
A takaddamar da ake yi dangane da shirin Nukiliyarta, Iran ta nuna shirin yin nazari akan tayin da kasashen ne biyar masu kujerun dindindin a MDD hade da Jamus suka yi mata. Ministan harkokin wajen Iran Manushir Mottaki ya fada a birnin Teheran cewa duk da haka dai kasarsa zata ci-gaba da inganta sinadarin uranium da take bukata. Ministan ya kara da cewa bai kamata a gindaya wasu sharudda ba kafin gudanar da shawarwari akan batun nukiliyar kasarsa. Da farko babban jami´in diplomasiyar kungiyar EU Javier Solana ya gargadi Iran da kada ta yi watsi da sabon tayin da aka yi mata. Ya ce idan ta yi haka, tamkar da akwai kwakkwarar shaidar cewar kasar na son ta kera makaman nukiliya ne amma ba makamashi ba.