An yi maraba da martanin da Iran ta mayar
June 17, 2006A takaddamar da ake dangane da shirin nukiliyar Iran, Amirka ta nunar da cewa an samu wata kyakkyawar alama daga birnin Teheran. A lokacin da ta ke magana a birnin Washington sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta yi fatan cewa yanzu Iran zata zabi hanyar ba da hadin kai. Da farko dai shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad ya bayyana tayin taimakon da kasashe masu zaunannun kujeru a kwamitin sulhu na MDD da kuma Jamus suka yi da cewa wani mataki ne na ci-gaba. Sannan a lokaci daya ya ba da sanarwar yin nazari sosai akan tayin. Kasashen masu ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhu hade da Jamus sun yi alkawarin bawa Iran jerin taimakon tattalin arziki da na fasahar samar da makamashi idan ta dakatar da aikin inganta sinadarin uranium.