1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi mummunan girgizan ƙasa a Iran

Usman ShehuApril 9, 2013

Hukumomin ƙasar Iran sun tabbatar da mutuwar mutane da yawa, kana da jikkata aƙalla mutane 800, biyo bayan girgizan ƙasa

https://p.dw.com/p/18CiX
Epizentrum Kaki nahe Bushehr. Richterskala 6.2 *** Rechteeinräumung: Lizenzfrei, pgnews.ir 9. April 2013
Daya daga cikin wadanda girgizan ƙasar Iran ya shafaHoto: pgnews.ir

A ƙalla mutane 30 suka mutu, wasu kimanin 800 suka jikkata, bayan girgizan ƙasa da ya faru kusa da tashar nukiliyan ƙasar Iran. Gwamnan jahar Bushehr inda lamarin ya faru, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace suna ci gaba da zaƙulo wadanda girgizar ta rutsa da su. Ƙasar Rasha wanda ke agazawa Iran a shirin mallakar nukiliya, ta ce koda yake girgizan ƙasar na da girma, amma bai shafi tashar nukiliyan ba. Ita ma hukumar kula da nukilya ta MDD wato IAEA, tace ƙasar Iran ta tabbatar musu da cewa, wannan girgizan ƙasar bata yi lahani ga na'urorin nukilya da ake da su ba. Lamarin dai ya faru ne da tazarar kilo mita 95 daga nisan tashar nukiliya da ke Bushehr.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mouhamadou Awal