1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: APC ta nemi kotu ta kori karar Peter Obi

Ramatu Garba Baba
April 12, 2023

Jam'iyyar APC ta nemi kotu da ta kori karar da dan takara na shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar Labour ya shigar don kalubalantar sakamakon zaben 2023.

https://p.dw.com/p/4PxXD
Peter Obi na jam'iyyar Labour
Peter Obi na jam'iyyar LabourHoto: Gbemiga Olamikan/AP/picture alliance

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi kira ga kotun daukaka kara da ke Abuja, da ta kori karar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Peter Obi ya shigar na kalubalantar sakamakon zaben kasar 2023 da ya zo na uku. Jam'iyyar ba ta ce komai a game da karar da dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya shiga na kalubalantar sakamakon zaben ba tukun na.

Sanarwar na zuwa a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, jami'an kula da shige da fice a Britaniya, sun tsare Mista Peter Obi a filin jirgin saman Heathrow da ke birnin Landan a lokacin da ya ke shirin barin kasar, Mista Obi ya iya barin kasar bayan amsa wasu tambayoyi daga jami'an. Tsohon gwamnan jihar Anambra da ya zo na uku a zaben ya yi ikirarin lashe babban zaben na 2023, ya zuwa karshen watan Mayu za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya.