1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na fuskantar harin yanar gizo

Abdourahamane Hassane
January 14, 2022

Gwamnnatin Ukraine ta sanar da cewar an kai mata hari ta yanar gizo a shafuka da yawa na gwamnatin  wanda ba a da masaniya daga inda aka yi fashin na intanet.

https://p.dw.com/p/45XKD
Symbolfoto | Cybersicherheit
Hoto: Frank Rumpenhorst/dpa/picture alliance

Hukumomin na Ukraine sun ce an gaza shiga shafukan ofishin ministan harkokin waje da na agajin jin kai da sauran manyan ma'aikatun gwamnatin a ranar Juma'a(14-12-21).To amma sun ce kawo yanzu  kwararru a kan sha'anin yanar gizon na kokarin gyarta lamarin. Ukraine da sauran kasashen yammacin duniya sun dade suna zargin Rasha da laifin kai harin a kan yanar gizonsu da nufin tatsar bayyanai daf da lokacin da ake kai ruwa rana tsakanin Rashar da kasashen.