Ghana: Kotu ta yi watsi da karar Mahama
March 4, 2021Talla
Kotun ta ce bangaren John Mahama da ke zargin an tafka magudi a yayin zaben, bai gabatar da wasu kwararan hujjojin da suka gamshi kotun ba, da zai sa har ta sake kiran wani sabon zaben shugaban kasa, saboda hakan kai tsaye ta yi watsi da karar.
Ba tun yau ba ne mutanen biyu da kowannensu ya shugabanci kasar Ghana ke ta ja in ja kan batun lashe zaben shugaban kasa, a kasar da ke da matukar tasiri a fagen dimukuradiyyar yankin yammacin Afirka.