1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pierre Nkurunziza ya zabi magajinsa

Usman Shehu Usman
January 26, 2020

Jam'iyya mai mulki a kasar Burundi ta zabi Janar Evariste Ndayishimiye a matsayin wanda zai yi mata takaran shugaban kasa a zaben kasar da zai gudana watanni hudu

https://p.dw.com/p/3Wpvo
Burundi Gitega -  President Pierre Nkurunziza  bei Wahlkampaqne
Hoto: E. Ngendakumana

Janar Ndayishimiye ya kasance babban na hannun daman shugaba Nkurunziza mai ci ne, wanda ya ce ba zai yi takara ba, bayan da sake takaransa ya jefa kasar cikin rikici tun a shekara ta 2015. Evariste Ndayishimiye dan shekaru 52 a duniya, ya taba rike mukamin ministan cikin gida da ministan tsaro, da kuma shugaban majalisar gamayyar ministocin soja da farar hula. Janar din na cikin wadanda suka taka rawa a kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a shekara ta 2003, wanda ya kawo karshen yakin basasa a kasar.