An zargi Jami'an Spain da tozarta bakin haure
February 8, 2014Mahukuntan kasar Spain sun karyata zargin da ake wa jami'an tsaronsu na harba harsashin roba a kan bakin haure da ke kokarin shiga kasar ta teku, bayan wasu 'yan Afirka tara sun nutse a ruwa a yunkuri makamancin haka.
A ranar Alhamis din nan ce dai mutane tara da suka hadar da mace guda suka rasa rayukansu, a kan hanyarsu ta isa garin Ceuta da ke Spain, ta cikin wani kogi da ke Morokko wadda ke makwabtaka.
Kafofin yada labaru da kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun ruwaito cewar, jami'an tsaron na Spain da na Morokko sun yi kokarin hana bakin hauren fita daga tekun zuwa garin na Ceuta.
Mahukuntan Spain din dai sun amince da amfani da harsasan roban a bangaren jami'an tsaron, sai dai a cewarsu harbin ban tsoro aka yi a sararin samaniya, amma ba a kan bakin hauren ba.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal