1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka sun yi biris da mamayar Rasha a Ukraine

Zainab Mohammed Abubakar MA
April 8, 2022

Wasu daga cikin jaridun Jamus sun yi nazari kan matsayin kasashen Afirka game da mamayar da Rasha ta kai wa Ukraine, abin kuma da a yanzu ga alama kowa ya soma ji a jikinsa

https://p.dw.com/p/49fRx
Äthiopien AU-Gipfel in Addis Abeba | Cyrial Ramaphosa übernimmt Vorsitz von Abdel Fattah al-Sisi
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Jaridar Der Freitag wadda ta buga labarinta mai taken "Kasashen Afirka da dama sun ki sukar mamayen da Rasha ta ke yi a Ukraine", ta ce jim kadan bayan afka wa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu, manyan jami'an sojin Rasha sun hada wata gagarumar liyafa a wani gida da ke kusa da birnin Pretoria. Jakada IlyaRogachev ne dai mai masaukin bakin wannan liyafar, kuma bakinsa sun hada da ministan tsaron Afirka ta Kudu Thandi Modise da hafsan sojin kasar, wanda bai soke goren gayyata kamar sauran kasashen ba.

Wannan dai ce irin ta shugabanni da gwamnatocin Afirka, wadanda da yawa ba su fito fili suka yi Allah wadai da mamayar ta Rasha ba. A lokacin da babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya zartas da wani kuduri na adawa da mamayar, kasashen Afirka sun kasance rabin kasashe 17 da suka kaurace. Daga cikin kuri'u biyar da aka ki amincewa har da na Eritrea.

Shugabannin mulkin soji a Sudan sun ji ba dadi lokacin da suka kusan ninka farashin burodi a bara saboda hauhawar farashin kayayyaki da faduwar darajar kudin kasar. Lokacin da gwamnatin da ta gabata ta yi wani abu makamancin haka shekaru uku da suka gabata, an yi zanga-zangar gama gari. A karshe dai wannan rikici ya janyo karshen mulkin sai madi ka ture na tsawon lokaci da shugaba Omar al-Bashir na Sudan din ya yi.

Unruhen im Sudan | Demonstration
Yadda a baya mata ke zanga-zanga saboda tsadar rayuwa a Sudan Hoto: Getty Images/AFP/E. Hamid

Miliyoyin mutane a Afirka da kasashen Larabawa na dogaro da burodi da masara a matsayin cimaka mai muhimmanci, don haka ne a siyasance a kan yi taka tsantsan da batutuwan da suka shafe su. Yakin da ake yi a Ukraine ya kara ta'azzara halin da ake ciki a Sudan da sauran kasashe masu rauni a Afirka. Kafin barkewar wannan rikici Sudan na samuun kashi daya daga cikin uku na hatsin da al'ummarta ke amfani da shi daga Rasha.  Kazalika kasar Ukraine ma babbar abokiyar cinikayya ce ta kayayyakin noma. Amma yanzu akwai ayar tambaya dangane da samun wadannan kayayyaki yayin da farashin kasuwannin duniya ke tashi matuka.

Sai yankin gabashin Afirka, inda jaridar Die Zeit ta yi nazari kan yadda sauyin yanayi da kuma annobar corona suka yi wa makiyayan Kenya illa, kuma a yanzu ke neman sabuwar rayuwa. Jaridar ta ci gaba da cewa gabashin Afirka na cikin fari, kuma tun daga faduwar daminar shekara ta 2020 babu wani abun a zo a gani da aka samu saboda karancin ruwan sama kamar yadda aka saba a baya. Baya ga arewaci da gabashin Kenya, wasu yankuna da dama na kasashen Habasha da Somaliya na fama da matsalar.

Dürre ohne Ende Am Horn von Afrika droht Hungersnot
Wasu ke nan tsaye suna kallon ta'adin da fari ya yi musu a gabashin AfirkaHoto: picture-alliance/dpa

Al'ummar Turkana, wadanda makiyaya ne sun san yadda suke tunkarar fari har na tsawon shekarar. Amma a bambancin da ke tsakanin wannan da wanda suka saba shi ne, a baya fari na faruwa ne duk bayan shekaru 10, ba kuma shekara biyu ko uku ba, kamar yadda ake gani a yanzu.

Sannan kuma tun cikin shekarata 2020, corona ta tilasta wa kasashen Afirka kafa dokar kulle na tsawon watanni. Likitocin dabbobi sun daina zuwa duba lafiyar dabbobi, sannan ma'aikatan lafiya sun daina zuwa yi wa yara allurar rigakafi. An daina kai musu garin fulawa da masara da shinkafa ko sikari. Tun daga nan, komai ya yi tsada. Yanzu, farashin kayan abinci ya kara yin tashin gwauron zabi saboda yaki da ya barke a can Turai mai tazarar dubbam kilomitoci wanda ya yi sanadiyyar karancin alkama da masara da kuma man girki.