An zargi Pakistan da hannu a rikicin Kunduz
September 29, 2015
A wannan Litinin din da ta gabata mayakan kungiyar Taliban suka samu nasara kwace garin Kunduz da ke zama birnin mai mahimmanci a yankin arewacin kasar, kuma karo na farko ke nan da suka samu nasarar kwace wani birni tun bayan kawo karshen mulkin kungiyar a shekara ta 2001, kimanin shekaru 14 da suka gabata kenan.
Yayin da mayakan gwamnatin ke neman sake kwato birnin na Kunduz daga hannun 'yan Taliban tuni wannan labarin ya dauki hankalin 'yan kasar ta Afghanistan har ma wani mutum mai suna Ali Akbar ke cewar "ina da yakinin cewa hukumar tsaron Pakistan ta na da hannu a cikin faduwar birnin Kunduz.
Yayin da wasu ke zargin gwamnatin Pakistan da hannu wajen faduwar Kunduz, wasu 'Yan Afghanistan kamar Hafizullah Khan mazaunin birnin Kabul fadar gwamnatin kasar na ganin lamarin da ya faru alama ce ta irin abubuwa da za su faru nan gaba don a cewarsa ''idan yanayin ya ci gaba, nan ba da jimawa ba yankuna 10 za su fada hannun kungiyar Taliban, shi ke nan mutanenmu da kasar sun sake shiga mawuyacin hali ke nan''.
Tuni mahukuntan Afghanistan suka tura sojoji da ke kusa da Kunduz domin taimakawa wajen sake kwato garin mai mahimmanci daga hannun kungiyar Taliban wadda ta daga tuta a tsakiyar birnin. Tuni Shugaba Ghani ya shawarci mutanen kasar da su ma su bada tasu gudunmawar wajen samun nasarar da aka sanya a gaba inda ya ke cewar "ina bukatar duk 'yan kasa su bayar da goyon bayan da ya dace ga jami'an tsaro".