1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makamin Rasha ya harbo jirgin Malesiya a Ukraine

Gazali Abdou Tasawa
May 24, 2018

Sakamakon bincike kan musabbabin faduwar jirgin Malesiya Airlines sanfarin MH17 a kasar Ukraine a shekara ta 2014, ya nunar da cewa an hari jirgin ne da wani makami mai lizzami na wata rundunar sojin Rasha.

https://p.dw.com/p/2yGZa
Flug MH17
Hoto: picture-alliance/AP Photo/P. Dejong

Sakamakon bincike kan musabbabin faduwar jirgin Malesiya Airlines sanfarin MH17 a kasar Ukrain a shekara ta 2014, ya nunar da cewa an hari jirgin ne da wani makami mai lizzami na sojin kasar Rasha. Wilbert Paulissen, jagoran masu aikin binciken ne ya bayyana haka a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a wannan Alhamis a kasar Holland inda ya ce sun samu alamu da dama da suka hada da shaidar sawun yatsun hannu da aka gano a saman makami mai lizzami mai suna Buk-Telar mallakar bataliya ta 53 ta sojin Rasha, abin da ya ba mu tabbacin cewa da wannan makami ne aka kakkabo wannan jirgi.

A ranar 17 ga watan Yulin 2014 ne dai wani makami ya kakkabo a sararain samaniyar kasar Ukraine jirgin na Malesiya Airlines dauke da fasinjoji 298 akasarinsu 'yan kasar Holland wadanda dukanninsu suka halaka. 

Da ma dai sakamakon binciken da aka gabatar a watan Satumban 2016 ya nunar da cewa makamin mai lizzamin da ya kakkabo jirgin na kasar Rasha ne ba tare da amma bayyana wadanda suka harbo makamin ba. A baya dai so tari Kasar Rasha ta sha musunta zargin harbo wannan jirgi.