An yi wa mutane hukuncin kisa a Iran
July 8, 2023Talla
Kafar yada labaran kasar mallakar gwamnati ta ruwaito cewar an rataye mutane biyu a gaban bainar jama'a a wani titi da ke birnin Chiraz bayan tabbatar ma su da laifin harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 a watan Oktoban shekarar 2022.
Wurin ibadar na Chah-Cheragh da mutanen suka kai wa harin a bara, na daya daga cikin hubbare masu matukar daraja ga mabiya mazhabar Shi'a.
Iran dai na a sahun farko na daidaikun kasashen duniya da har yanzu suke zartar da hukuncin kisa duk da irin gwagwarmayar da kungiyoyin kare hakkin dan Adam ke yi don ganin an kawo karshen wannan al'ada.