1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ƙaddamar da bikin rantsar da shugaban ƙasar Togo

May 3, 2010

An rantsar da shugaba Faure Yassimbe Eyadema na ƙasar Togo,shugabannin ƙasashen Afirka da dama suka halarci bikin

https://p.dw.com/p/NDgZ
Shugaban ƙasar Togo Faure Yassimbe EyademaHoto: DW

An gudanar da bikin rantsar da shugaban ƙasar Togo Faure Yassimbe Eyadema a yau a Lome babban birnin ƙasar a gaban kotun tsarin mulki ta ƙasar, tare da halarta kimanin mutane kamar dubu takwas. Daga cikin waɗanda suka halarci bikin har da shugabannin ƙasashen Ghana, Benin Kote- Divuar da kuma Burkina Faso.

Mista Faure Eyadema wanda ya samu kashi 60,88 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a cikin watanni ukku da suka gabata ya sha kira ga 'yan adawar ƙasar da su rungumi ƙaddara tare da mai da hankali ga aikin gina ƙasar.

Babu dai ɗaya daga cikin 'yan adawar da ya halarci bikin ratsuwar wanda tun bayan bayyana sakamakon zaɓen suka shiga yin zanga zanga. Wannan kuma shi ne karo na biyu ke nan da mista Faure ya ke samun nasara a zaɓen shugaban ƙasar da ƙungiyar adawa ta kira haramtacce saboda maguɗin da ta ce an tabƙa.

Mawallafi: Abdurrahmane Hassane

Edita: Mohammad Nasiru Awal