Ana ci gaba da hare hare a Pakistan
July 19, 2007Talla
Akalla mutane 34 ne suka rasa rayukansu cikin wani harin kunar bakin wake a kasar Pakistan.An kai harin ne kann wasu yan kasar China da jamian tsaro na Pakistan a garin Hub na lardin Baluchistan.
A wani harin na dabam kuma akalla mutane 8 suka rasa rayukansu wasu kuma 29 suka samu raunuka yayinda bam ya fashe a bakin hedkwatar horasda yan sanda a arewa maso yammacin kasat.